Koriya Ta Arewa Ta Gwada Makamin Nukiliya Mafi Girma
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10801-koriya_ta_arewa_ta_gwada_makamin_nukiliya_mafi_girma
Koriya ta Arewa ta sanar da cewa tayi nasara gwada wani makamin nukiliya mafi girma da bata taba yin irinsa ba a yau Juma'a
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 09, 2016 01:08 UTC
  • Koriya Ta Arewa Ta Gwada Makamin Nukiliya Mafi Girma

Koriya ta Arewa ta sanar da cewa tayi nasara gwada wani makamin nukiliya mafi girma da bata taba yin irinsa ba a yau Juma'a

Wannan dai shi ne karo na biyar da kasar ke yin irin wannan gwajin, tun bayan wani da ake ganin shi ne mafi karfi a watan fabrairu shekarun 2013.

Gidan talabijin din kasar ya nuno wata mai gabatar da shirye shirye na cewa wannan gwajin shi ne irinsa mafi karfi da da kasar tayi karkashin jagorancin shugaba Pyongyang. 

Ta ce masana kimiya na kasar sunyi nasara a wannan sabon gwajin a cibiyar nukiliya dake arewacin kasar.

kafin hakan dai bayanai daga makofciyyar kasar wato Koriya ta kudu sun ce an ji karfin gwajin daya hadasa girgiza kasa da karfin maki 5,3.

A nata bangare shugabar kasar Koriya ta kudu Park Geun-hye ta yi tur da wannan gwajin tana mai cewa babbar barazana ce ga tsaro a yankin kana kuma hakan ya keta dokokin kwamitin tsaro na MDD da kuma kasa da kasa.

Shi ma a nasa bangare firaministan kasar Japon Shinzo Abe ya ce ya yi allawadai da wannan gwajin yana mai cewa ba abinda za'a amunce dashi ba ne.

An dai jima ana tsaurara takunkumai iri daban daban ga koriya ta Arewa akan irin wannan gwajin saidai ba tare da hakan ya katse mata hamzari ba.