Amurka ta kara yawan Sojojin ta A kasar Iraki
Majiyar tsaron Amurka ta sanar da kara yawan Sojojin ta dake Iraki
Kamfanin dillancin labaran Faransa daga birnin Watsinton ya nakalto John Dorian kakakin hukumar yaki da ta'addancin Kungiyar IS na cewa a cikin 'yan kwanakin da suka gabata Amurka ta tura sojoji 400 zuwa kasar Iraki,inda adadin sojojin Amurkan dake kasar ya haura zuwa dubu 4 da 460.
Kasar Amurka na kara yawan Sojojin ta ne a kasar ta Iraki yayin da Dakarun tsaron kasar da na kai ke fatatakar 'yan ta'addar na IS da suka mamaye wani bangaren kasar tun shekaru biyun da ta gabata, 'yan ta'addar IS din dai na samun goyon bayan Amurka da wasu kasashen Larabawa na yankin da kudu da makamai, amma duk da hakan tun daga shekarar 2014 kasar Amurka ta fara kai hare-hare ta sama a kasashen Iraki da Siriya da nufin yaki da ta'addanci.