Amurka Na Juyayin Harin 11 ga Watan Satumba
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10891-amurka_na_juyayin_harin_11_ga_watan_satumba
Yau Lahadi, Amurkawa na juyayin sheraru 15 da aukuwar harin 11 ga watan Satumba 2001.
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 11, 2016 06:16 UTC
  • Amurka Na Juyayin Harin 11 ga Watan Satumba

Yau Lahadi, Amurkawa na juyayin sheraru 15 da aukuwar harin 11 ga watan Satumba 2001.

A bikin da aka shirya yau a New York don tuni da wannan rana za'a bayyana sunayen wadanda suka mutu a hare-haren.

Ana sa 'yan takara a zaben shugabancin kasar  Hillary Clinton da Donald Trump zasu halarci bikin.

Kimanin mutane 3,000 ne suka hallaka a harin da kungiyar 'Al-Qaïda ta kai ta hanyar jiragen sama bayan garkuwa dasu, suka kuma aukawa mayen gine ginen World Trade Center a birnin New York da Pentagone a kusa da birnin Washington da kuma lardin Pennsylvanie a Shanksville.

Harin 11 ga watan Satumban 2001 shi ne na farko kuma mafi muni da aka kaiwa Amurka a cikin shekaru kusan 200.