Obama Ya Kaddamar Cibiyar Tarihin Bakar Fatan Amurka
Shugaba Barack Obama, ya kaddamar a hukumance bude cibiyar tarihi da al'adu na bakar fatan Amurka a birnin Washington, a a daidai lokacin da cin zarafi da kuma kyammar bakaken fata ke kara kamari a wannan kasa.
Da yake magana a bikin kaddamar da cibiyar, Obama yace "Galibi muna manta miliyoyin Amurkawa, wadanda suma hakika suna cikin tarihin gina kasan nan"
Mr. Obama ya kara da cewa cibiyar, zata bada labarin Amurka wanda hakan zai taimakawa wajen karfafa sulhu a zukatun al'umma.
Cikin wadanda suka halarci bikin a jiya Asabar harda tsohon shugaban kasar George Bush karami, wanda ya sanya hanu kan dokar da ta bada izirnin a fara aikin ginin cibiyar,da kuma dan majalisar wakilan Amurka mai wakiltar jahar Georgia, John Lewis, wanda har wayau, gwarzo ne a fagen yaki da kare 'yancin tsiraru,
A baya bayan nan dai Amurka na shan suka dangane da ci karuwar kyammar bakaken fata, musamen kan kashewa da jami'an Sanda keyi masu.