Amurka : An Cafke Mutumin Da Ya Kai Hari A Washigton
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11536-amurka_an_cafke_mutumin_da_ya_kai_hari_a_washigton
'Yan sanda a Amurka sun sanar da cafke dan bindigan daya hallaka mutane biyar a wata cibiyar kasuwanci dake arewa maso yamancin birnin Washington.
(last modified 2018-08-22T06:58:59+00:00 )
Sep 25, 2016 02:15 UTC
  • Amurka : An Cafke Mutumin Da Ya Kai Hari A Washigton

'Yan sanda a Amurka sun sanar da cafke dan bindigan daya hallaka mutane biyar a wata cibiyar kasuwanci dake arewa maso yamancin birnin Washington.

Kakakin 'yan sanda yankin ne, Mark Francis, ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a wannan Asabar.

Mutane biyar ne da suka hada da mata hudu da namiji guda suka mutu a yayin da dan bindigan ya bude wuta a cibiyar kasuwancin Cascade Mall dake lardin Burlington a ranar Juma'a data gabata.

Kawo yanzu 'yan sanda yankin sun ce babu wani abu dake nuna cewa alamar ta'addanci a cikin lamarin.

Masu binciken dai sun nuna hoton bidiyon maharin dan shekaru kimanin shekaru ashirin, wanda har yanzu suka ce basu san manufarsa ba.

Shi kuwa a nasa bangare magajin birnin, Steve Sexton ya nuna matukar damuwarsa dangane da ire-iaren wadanan hare-haren dake shafar kasarsa inda kowa yake da incin mallakar bindiga.