Hillary Clinton Ta Jaddada Aniyarta Ta Na Goyon Bayan H.K.Isra'ila
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11599-hillary_clinton_ta_jaddada_aniyarta_ta_na_goyon_bayan_h.k.isra'ila
Yar takarar shugabancin kasar Amurka a jam'iyyar Democratic Hillary Clinton ta jaddada aniyarta ta kare munanan manufofin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila idan ta yi nasarar dare kan karagar shugabancin Amurka.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 26, 2016 07:24 UTC
  • Hillary Clinton Ta Jaddada Aniyarta Ta Na Goyon Bayan H.K.Isra'ila

Yar takarar shugabancin kasar Amurka a jam'iyyar Democratic Hillary Clinton ta jaddada aniyarta ta kare munanan manufofin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila idan ta yi nasarar dare kan karagar shugabancin Amurka.

Jaridar Yahudawan Sahayoniyya ta Haerez ta habarata cewa a ganawar tada gudana tsakanin fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Netanyahu da Hillary Clinton 'yar takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Democratic ta jaddada masa cewa; Idan har ta samu nasarar dare kan karagar shugabancin Amurka, to ba zata taba barin a mika batun rikicin Yahudawan Sahayoniyya da Palasdinawa zuwa gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ba,ballantana har a kai ga batun fitar da kuduri da zai takurawa Yahaudawan Sahayoniyya. 

Har ila yau Hillary Clinton ta jaddada aniyarta ta goyon bayan shirin kafa kasar Palasdinu bisa daidaiton bakin Hukumar Palasdinawa da gwamnatin haramtacciytar kasar Isra'ila ko kuma bisa mahangar bangare guda wato Yahudawan Sahayoniyya.