Mutanen Kolombiya Sun Ki Amincewa Da Yarjejeniyar Sulhu Da Kungiyar FARC
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11905-mutanen_kolombiya_sun_ki_amincewa_da_yarjejeniyar_sulhu_da_kungiyar_farc
Rahotanni daga kasar Kolombiya sun bayyana cewar al’ummar kasar sun ki amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar ta kulla da ‘yan tawayen FARC da nufin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru 52 ana fafatawa a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:01+00:00 )
Oct 03, 2016 08:28 UTC
  • Mutanen Kolombiya Sun Ki Amincewa Da Yarjejeniyar Sulhu Da Kungiyar FARC

Rahotanni daga kasar Kolombiya sun bayyana cewar al’ummar kasar sun ki amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar ta kulla da ‘yan tawayen FARC da nufin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru 52 ana fafatawa a kasar.

Rahotannin sun bayyana cewar sakamakon zaben raba gardamar da aka gudanar a kasar kan wannan batun ya nuna cewa sama da kashi 50.21 cikin dari na ‘yan kasar ba su amince da yarjejeniyar ba, yayin da kashi 49.78 cikin dari kuma suka amince da ita.

Shugaban kasar da masu goyon bayan yarjejeniyar sun yi fatan za ta samu karbuwa a wajen al'ummar kasar,  to sai dai sakamakon zaben yana a matsayin wata koma baya ga kokarin shugaban kasar Juan Manuel Santos na cimma sulhu da zaman lafiya da 'yan tawayen FARC din bayan yarjejeniyar sulhun da ya sanya wa hannu tare da shugaban 'yan tawayen Timoleon Jimenez a ranar 26 ga watan Satumba.

Shugaba Santos ya bayyana cewar duk da sakamakon kuri'ar raba gardamar amma dai zai ci gaba da wannan kokari na sa na cimma sulhu da 'yan tawayen har zuwa karshen wa'adin mulkinsa.