Zaben, António Guterres, A Matsayin Sabon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
A ranar Alhamis din da ta gabata ce, membobin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya suka zabi tsohon firayi ministan kasar Portugal Antonio Guterres a matsayin sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
A makon da ya wuce ne kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniyan ya gabatar da sunan Antonio Guterres a matsayin dan takarar kujerar babban sakataren MDD don maye gurbin sakataren na yanzu Mr. Ban Ki Moon wanda wa'adin mulkinsa zai kare a ranar 31 ga watan Disamban wannan shekarar (2016).
Mr. Guterres dan shekaru 67 a duniya, wanda shi ne zai zama babban sakataren majalisar na tara ya rike mukamin firayi ministan kasar Portugal daga shekarar 1995 zuwa 2002 sannan kuma ya rike babban kwamishinan Majalisar Dinkin Duniyan kan lamurran 'yan gudun hijira har na tsawon shekaru 10 wato daga shekara ta 2005 zuwa 2015.
Tabbas akwai kalubale masu yawan gaske a gaban sabon babban sakataren MDD, daga cikinsu kuwa shi ne batun sauya tsarin wannan cibiya ta kasa da kasa musamman tsarin kwamitin tsaron majalisar wanda kasashen duniya da dama sun jima suna kuka kan hakan da kuma lamarin kasafin kudin gudanar da majalisar. Don kuwa cikin shekarun baya-bayan nan MDD ta fuskanta kuma tana ci gaba da fuskantar mummunan suka musamman a fagen tsarinta, ayyukanta, irin karfin da membobinta suke da shi da kuma hanyoyin samun kudinta.
Ko shakka babu yin kwaskwarima ga tsarin majalisar wanda ya samo asali daga zamanin yakin ruwan sanyi sannan kuma ba ta tafiya daidai da yanayin da duniya take ciki a halin yanzu yana daga cikin mafiya muhimmancin lamurra a irin yanayin da duniya take ciki da ake ci gaba da samun sauyi cikin yadda duniya take gudana; musamman ma tsarin gudanarwa da ake amfani da shi a Kwamitin tsaron MDD da kasashe da dama suke kokarin ganin an sauya shi, shi din ma musamman irin karfin da wasu kasashe masu kujeran dindindin a kwamitin suke da shi.
Wani bangaren kuma da MDD take fuskantar suka da kuma kalubale shi ne bangaren inda majalisar take samun kudaden shiga da take gudanar da ayyukanta. Majalisar dai tana samun kudaden ayyukanta ne daga kudaden da kasashe membobin majalisar suke bayarwa. Abin da kowace kasa take bayarwa kuwa ya danganta ne da irin kudaden shigar da suke samu. A saboda haka ne Amurka ta zamanto ita ce kan gaba wajen samar wa majalisar da kudaden shigarta, sai kuma sauran kasashe su biyo baya. Don haka a fili yake cewa manyan kasashen duniya da suka ci gaba da fagagen masana'antu su ne kan gaba wajen ba da kudaden shigar majalisar, sauran kananan kasashe da masu tasowa kuwa abin da suke bayarwa bai taka kara ya karya ba. To amma duk da hakan Amurka ta kasance daga cikin kasashen da aka fi bin su bashi, don haka ne wasu suke ganin kin biyan wadannan kudaden da Amurkan ta ke yi wata siyasa ce ta yin matsin lamba ga majalisar don cimma manufarta ta siyasa.
Duk da cewa akwai yiyuwar rashin biyar kudaden da wasu kasashe suke yi wa MDD yana da alaka da matsalar tattalin arzikin da duniya take fuskanta, amma dai wasu kasashen suna amfani da hakan ne don yi matsin lamba ga majalisar don cimma wasu manufofinsu na siyasa, babban misalin hakan kuwa shi ne abin da kasar Saudiyya ta yi a kwanakin baya lokacin da babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya zarge ta take hakkokin kananan yara a kasar Yemen.
Dukkanin wadannan abubuwa suna daga cikin abubuwan da wasu kasashe suke bukatar yin kwaskwarima ga tsarin majalisar dinkin duniyan wasu ma har suke ganin hatta helkwatarta ma a daga shi daga birnin New York na Amurkan zuwa wata kasa ta daban mai tasowa.