Matan Amurka sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Donald Trump
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12652-matan_amurka_sun_gudanar_da_zanga_zangar_kin_jinin_donald_trump
Bayan watsuwar kalaman batsa da Dan takarar shugaban kasa na Amurka Donald Trump ya yi , Matan kasar sun gudanar da zanga-zanga a yankuna da dama domin bayana adawar su da shi.
(last modified 2018-08-22T06:59:06+00:00 )
Oct 19, 2016 03:09 UTC
  • Matan Amurka sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Donald Trump

Bayan watsuwar kalaman batsa da Dan takarar shugaban kasa na Amurka Donald Trump ya yi , Matan kasar sun gudanar da zanga-zanga a yankuna da dama domin bayana adawar su da shi.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya Talata Matan Amurka a gariruwan Chicago da Philadelphia sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawar su kan kalamar cin mutunci ga Mata da Mista Donald Trump dan takarar shugabancin kasar kalkashin jami'iyar Repablicain ya yi, mahalatar zanga-zangar sun bayyana cewa bai kamata ba suna da shuhura ta baiwa Mista  Trump damar fadar dukkanin abinda ya ga dama a kan  Mata.

Har ila yau mahalarta zanga-zangar sun zargi Donald Trump da ingata tare da watsa al'adar cin mutuncin Mata a Duniya.

A ranar Litinin din da ta gabata Matan birnin New York ma sun gudanar da irin wannan zanga-zanga ta kin jinin Donald Trump.