'Yan Takarar Shugabancin Kasar Amurka Sun Tafka Muhawara
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12691-'yan_takarar_shugabancin_kasar_amurka_sun_tafka_muhawara
'Yan takarar shugabancin kasar Amurka sun tafka muhawara a tsakaninsu a zagaye na karshe wadda aka kammala kimanin sa'a guda da ta gabata.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Oct 20, 2016 02:18 UTC
  • 'Yan Takarar Shugabancin Kasar Amurka Sun Tafka Muhawara

'Yan takarar shugabancin kasar Amurka sun tafka muhawara a tsakaninsu a zagaye na karshe wadda aka kammala kimanin sa'a guda da ta gabata.

A yayin muhawar 'yar takarar shugabancin Amurka a karkashin inuwar jam'iyyar Democrat Hillary Clinton, ta zargi dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump da mara baya ga shugaba Putin na Rasha, kan abin da ta kira bincike da  leken asiri da yake yi musu ta hanyar shafin wikileaks, yayin da Trump ya ce Putin ya shafi shugabannin fadar white House, yana mai ishara da Barack Obama, inda ya ce Putin yana da tasiri a yankunan da ke karkashin ikonsa agabas ta tsakiya, musamman a Syria.

Haka nan kuma Trump ya zargi Clinton da hannu a muggan laifuka, wadanda aka samu bayanan hakan a cikin wasikunta na email, wanda ta yi sauri ta goge su domin tsoron fallasa ta a idon Amurkawa, Trump ya ce Clinton ta share irin wadannan wasikun fiye da dubu 33 daga cikin email nata, wanda hakan ke nuni da rashin gaskiya.