Damuwar Kasar Faransa Kan Shigar Yan Ta'adda Nahiyar Turai Daga Libya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i127-damuwar_kasar_faransa_kan_shigar_yan_ta'adda_nahiyar_turai_daga_libya
Ministan tsaron kasar Faransa ya bayyana damuwarsa da yiyuwan yan ta'adda daga kasar Libya su shiga kasashen turai.
(last modified 2018-08-22T06:57:44+00:00 )
Feb 02, 2016 07:23 UTC
  • Damuwar Kasar Faransa Kan Shigar Yan Ta'adda Nahiyar Turai Daga Libya

Ministan tsaron kasar Faransa ya bayyana damuwarsa da yiyuwan yan ta'adda daga kasar Libya su shiga kasashen turai.

Ministan tsaron kasar Faransa ya bayyana damuwarsa da yiyuwan yan ta'adda daga kasar Libya su shiga kasashen turai. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Jean-Yves Le Drian yana fadar haka a jiya litinin. Ya kuma kara da cewa kasar Libya wacce bata da tsayayyen gwamnati tun bayan kifar da gwamnatin Mu'ammar Kazzafi ta zama barazana ga kasashen Turai don damar da yan ta'adda suka samu na rashin tsayeyyen gwamnati a kasar yasa suka kwace ikon da yankunan kasar.

Jean-Yves Le Drian ya ce a halin yanzu kungiyoyin yan ta'adda da dama sun sami wurin zama a kasar Libya. Kungiyar Daesh kadai tana iko da yankin na bakin ruwa mai tsawon killomita 300.

A makon da ya gabata ne gwamnatin kadar ta Faransa ta tattauna da gwamnatin kasar ta Libya wacce kasashen duniya suka amince da ita kan yakar yan ta'adda da suke kara samun karfi a kasar sanadiyyar yakin basasan da kasar ta fada ciki.

Kasashen duniya musamman na Afrika da Turai suna takurawa bangarorin da suke yakar juna a kasar Libya don kafa gwamnatin hadin kan kasa wacce zata bawa kasashen duniya damar yakar kungiyoyin yan ta'adda da suka maida kasar wata aljanna a garesu.