Yadda Kasashen Afrika Ke Juyawa Kotun ICC Baya
Kotun hukunta manya laifuka ta duniya ta shiga tsaka mai wuya a daidai lokacin da take fuskantar janyewar wasu kasashen Afrika mambobinta.
Ye zuwa yanzu kasashen Afrika uku ne suka dau matakin fucewa daga kotun, bayan da kasar Gambiya ta sanar da anniyar ta na juyawa kotun ta ICC baya.
Da yammcin jiya ne dai kasar Gambiya ta bakin ministan yada labaren kasar Sheriff Bojang ta sanar da anniyar ta na janyewa daga kotun.
A cikin sanarwar da aka karanta a gidan talabijin kasar wace kuma aka yada a shafukan sada zumunta, Mista Bojang ya zargin kotun ta ICC da yiwa kasashen Afrika bita da kuli musamen shugabanninta, alhali kuwa a cewarsa akwai kasashen yamma kusan talatin da suka tafka laifukan yaki tun bayan kafa wannan kotun aman babu wata damuwa a garesu.
Mista Bojang ya kara da cewa kasarsa ta jima tana kalubalantar kotun ta ICC musamen kan ta gurfarar da wasu kasashen yamma akan mutuwar dubban bakin haure 'yan Afrika a tekun Bahar Rum, saidai babu wani abu da kotun tayi.
Don haka a cewarsa daga ranar 24 ga watan na na Oktoba kasar bata zamen mamba a kotun, kuma tuni suka dau matakan ficewa a kotun kamar yadda hanyoyin janjewa suka tanada.
Wannan matakin ficewar kasar Gambiya daga kotun ta ICC, babban kalubale ne ga shugabar kotun, Fatu Bensuda, wace 'yar asalin kasar Gambiya ce kana tsohuwar ministar shari'a ta shugaba Yahya Jammeh.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kasashen Burundi da Afrika ta Kudu suka dau mataki makamancin wannan.
Kasar Burundi dai wadda ta fada cikin rudanin siyasa tun shekarar da ta gabata ta 2015 lokacin da shugaban ya dauki matakin neman wa'adi na uku na mulki, ta harzika ne sakamakon matakin MDD na neman bincike kan kisan kimanin mutane 450.
Ita kuwa Afrika ta Kudu matakin ficewar ta dai ya fito fili akan irin halin tsaka-mai-wuyar da kasar ta fuskanta a bara a lokacin da aka hura mata wuta a kan sai ta kama shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a yayin wani taron kungiyar Tarayyar Afrika a birnin Johannesburg.
Ko baya ga wadanan kasashen uku, akwai, Kenya da Nimibia da suka nuna alamun janye wakilcinsu a kotun.
Kasashen Afrika dai sun jima suna sukar kotun ICC da aka kafa a shekara 2002 wacce suke ganin ta koma tamkar Karen farautar kasashen yammaci akan shugabannin Afrika.
Duk da ‘Yar Afrika ce shugabar kotun amma shugabannin na ganin kotun ta fi mayar da hankalinta akan su sabanin wasu shugabannin duniya da suka aikata laifukan yaki musamman ta’asar da aka yi a Iraqi zamanin yaki da Saddam Hussain.
A halin da ake ciki dai babban sakatare na MDD, Ban ki Moon da shugaban majalisar kasashen da suka amunce da yarjejeniyar kafa kotun, ministan shari'a na Senegal Sidiki Kaba sunyi kira ga kasashen dake da korafe korafe akan kotun da kada su fice, tare da kira gare su dasu warware sabanin ta hanyar tattaunawa da sauren mambobin kotun.