Putin: Amfani Da Makamin Nukiliya Yana Nufin Karshen Duniya
Oct 28, 2016 15:26 UTC
Shugaban Kasar Rasha, ya bukaci a kawo karshen yaduwar makaman Nukiliya.
Vilademir Putin ya bukaci da a yi amfani da tsarin da ake da shi na hana yaduwar makaman Nukiliya a duniya, sannan ya kara da cewa: Amfani da makaman Nukiliya yana nufin karshen duniya.
Shugaban na kasar Rasha wanda ya gana da manema labaru ya ce; Nuna kwanji da makamin Nukiliya ba abu ne da za a mince da shi ba, kuma wani abu ne wanda Rasha ba za ta amince da shi ba.
Fadar Kiremalin ta kasa Rasha ta ce; A yayin taron manema labarun na yau juma'a wanda shugaban kasar ya yi, ya ci gaba da cewa; Wajibi ne ga kasashen da su ke da makaman Nukiliya a duniya da su zama masu sanin ya kamata.