Amnesty Ta Zargi 'Yan Sanda Italiya Da Muzgunawa Bakin haure
https://parstoday.ir/ha/news/world-i13315-amnesty_ta_zargi_'yan_sanda_italiya_da_muzgunawa_bakin_haure
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta zargi 'yan sanda Italiya da muzgunawa bakin haure.
(last modified 2018-08-22T06:59:10+00:00 )
Nov 03, 2016 02:51 UTC
  • Amnesty Ta Zargi 'Yan Sanda Italiya Da Muzgunawa Bakin haure

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta zargi 'yan sanda Italiya da muzgunawa bakin haure.

A rahoton data fitar kungiyar ta 'yan sanda na Italiya na amfani da hanyoyin da basu dace ba na muzgunawa bakin hauren musamen ta wajen hanyoyin da suke dauka wajen daukan alamun yatsosun hannuwansu.

Kungiyar ta Amnesty dai ta dora alhakin hakan ga kungiyar tarayya turai ta EU.

Amnesty ta ce saboda matsin lamba da kungiyar EU take yi wa Italiya na ta dau tsauraren matakai kan bakin hauren da 'yan gudun hijira shi ne yasa ake azabatawa bakin hauren irin haka.

Daga cikin wadanda kungiyar ta Amensty ta zanta dasu,15 sun ce sun sha duka sosai da kulkin 'yan sanda sanan ana manna masu na'urar nan ta 'yan sanda mai aiki da wutar lantarki.