Maida Martani a ciki da wajen Amerika Kan Zaben Donal Trump
https://parstoday.ir/ha/news/world-i13666-maida_martani_a_ciki_da_wajen_amerika_kan_zaben_donal_trump
Bayan an bada sanarwan zaben Donal Trump a matsayin shugaban kasar Amurka na 45 mutane daga ciki da wajen kasar sun yi ta nuna fushinsu a yayinda wasu kuma suke farin ciki a ciki da wajen kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:13+00:00 )
Nov 10, 2016 03:17 UTC
  • Maida Martani a ciki da wajen Amerika Kan Zaben Donal Trump

Bayan an bada sanarwan zaben Donal Trump a matsayin shugaban kasar Amurka na 45 mutane daga ciki da wajen kasar sun yi ta nuna fushinsu a yayinda wasu kuma suke farin ciki a ciki da wajen kasar.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa masu goyin bayan Hillary Clinton na jam'iyyar Democrate sun yi ta kona tutar Amerika da kuma wuraren zuba shara a kan tituna.

A cikin wasu hotunan da aka nuna a shafuffukann sadarwa na yanar gizo sun nuna cewa mutane a jihar Oregon sun hau kan titu a biranen jihar suna furta kalomin rashin amincewa da sakamakon zaben da kuma kone kone wuraren tattara shara.

Har'ila yau daliban Jami'a a jihar ta Orego wadanda suka yi fushi da sakamakon zaben sun fito kan titunan jihar da ta mummunan kalmomi da kuma kona wuraren zabu shara.

Banda haka a birnin Portland na jihar ta Oregon daruruwan mutane sun fito kan tituna suna ta zajin zabebben shugaban Donal Trump da kuma bayyana cewa yana da halayen nuna wariya.

Sai kuma a birnin Washington babban birnin Kasar masu goyon bayan Trump ta kuma yan adawa sun yi ta zagin juna a wani dandanli kusa da fadar White House sannan bayan wani lokaci suka shiga dokan juna wanda ya jawo shiga yansanda a tsakanin don rabawa.

A bangaren tattalin arziki kuma nasarar da Trump ya samu a zaben na shekaran jiya ya jawo faduwar hannayen jari a kasashen turai da Asia. A birnin Mosco kuma kasuwannin hannun jari sun yo kasa a jiya 10 ga watan Nuwamba bai sanarwan nasarar da Trump ya samu a zaben shugaban kasa na Amurka.

Cibiyar hannayen jari na RTS wacce ake saidasu da dalar amurka sun yo kasa da kasha 1% sai kuma kasuwar Micex a birnin Mosco wanda shima ya fadi da kasha 0.73%.

Har'ila yau farashin dala da kuma Euro idan an kwatanta da Rubel sun fadi kadan bayan nasar Donal Trump a zaben na shekaran jiya.

Labaran daya yake a birnin Londan na kasar Britania da kuma Tokyo na kasar Japan.

Sai kuma a bangaren siyasa inda Ewald Nowotny wani directa a babban bankin tarayyar Turai ya bayyana cewa bayan zaben Trump kan kujerar shugaban Amurka duniya zata shiga rashin tabbas na wani lokacin kafin a san yadda kama ludayinsa shugabancinsa zai kasance.

Nowotny ya kara da cewa bankin tarayyar Turai zata sanya ido ta ga irin sauye sauyen da za'a samu don daukar matakan da suka dace.

A nashi bangaren shugaban kasar Faransa Fransua Holand ya ce zaben Trump zai sauya al-amura da dama a duniya, kuma zai jefa fargaba a cikin al-amura da dama a bangaren tattalin arziki da sayasa a duniya.

Sai kuma Francois Bayrou shugaban jam'iyyar  Democrat ta kasar faransa ya ce zaben Trump zai haifar da matsalolin zamantakewa a kasar Amurka.

Sai kuma kasar Cuba inda gwamnatin kasar ta bada sanarwan rawan daji na sojojinta na tsawon kwanaki biyar a mako mai zuwa bayan nasarar da Trump ya samu a zaben na shugabancin Amurka.

Donal John Trump ya sami delegate 289 daga jihohin Amurka 50 a zaben na ranar Talata wanda ya bashi damar zama shugaban kasar Amurka na 45. A yayinda abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton na Jam'iyyar Democrate ta sami delegats 218 a zaben.

Banda haka jam'iyyar ta Republican ta sami kujeru 51 cikin 100 na majalisar dattawan kasar, sai kuma a majalisar wakilai inda ta sami kujeru 235 ta sami, a yayinda jam'iyyar Democrate take da 189.