Kasar Canada Ta Bukaci A kawo Karshen Rikicin Kasar Habasha.
(last modified Tue, 15 Nov 2016 12:03:23 GMT )
Nov 15, 2016 12:03 UTC
  • Kasar Canada Ta Bukaci A kawo Karshen Rikicin Kasar Habasha.

Canada Ta Bukaci A Daina Rikici A Habasha.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Canada ta yi kira ga kasar Habasha da ta kawo karshen tashe-tashen hankulan da su ke faruwa a cikin yankun Amhara da Oromo.

Bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Habasha ta fitar a yau litinin ya yi ishara da ganawar da aka yi a tsakanin Piraminstan kasar Stephane Dion da takwaransa na Habasha Hailemariam Desaleng, sannan kuma ya jaddada wajabcin  baiwa yan kasar hakkokinsu, musamman ma dai samari, domin tabbatar da ci gaba mai dorewa a kasar ta Habasha.