Ana Ci Gaba Da Hana Musulman Kasar Myanmar Hakkokinsu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i13987-ana_ci_gaba_da_hana_musulman_kasar_myanmar_hakkokinsu
Har yanzun jami'an tsaron kasar Myanmar suna ci gaba take hakkin musulman kasar musamman a lardin Rakhin. Ofishin jami'an sojojin kasar Myanmar ya bayyana cewa yana tana binciken wadanda suka kai hare hare kan ofisoshin yansanda a cikin watan Octoban da nuwamba na wannan shekara suka kuma kashe mutane 69 sannan suka raunata wasu 234.
(last modified 2018-08-22T06:59:15+00:00 )
Nov 16, 2016 11:46 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Hana Musulman Kasar Myanmar Hakkokinsu

Har yanzun jami'an tsaron kasar Myanmar suna ci gaba take hakkin musulman kasar musamman a lardin Rakhin. Ofishin jami'an sojojin kasar Myanmar ya bayyana cewa yana tana binciken wadanda suka kai hare hare kan ofisoshin yansanda a cikin watan Octoban da nuwamba na wannan shekara suka kuma kashe mutane 69 sannan suka raunata wasu 234.

Banda haka masu tsatsauran ra'ayin addinin buda sun kona gidagen musulman yan Rakhin da dama. Banda haka a wani bangaren jami'an tsaron kasar ta Myanmar sun budewa wadan nan masu tsatsauran ra'ayin addini wurare don kissan musulman na kabilar Rohinga. Kamar yadda suka sukan kashe musulman tare da tuhumarsu da ayyukan ta'addanci da kuma alaka da yan ta'adda daga wajen kasar.

Majiyar labarai daga yankin na Rashin sun bayyana cewa sojojin kasar ne suke budewa masu tsatsaurar ra'ayin addini hanyoyi da kuma damar kona gidajen musulman Rohinga.

Sai kuma a bangaren gwamnatin kasar wacce taki amincewa da yan kabilar ta Rohinga a matsayin yan kasa don haka basa da hakkin samun kome daga bangaren gwamnatin kasar wadanda suka hada da karatu da kula da lafiyan. Musulman kasar ta Myanmar dai sun kasance cikin takurawa na jami'an tsaron kasar da kuma masu tsatsauran ra'ayin addinin na fiye da shekaru 4 da suka gabata.

Sannan wani abin mamaki shi ne duk abubuwan da suke faruwa a cikin yan shekaru da suka gabata suna faruwa ne a idon jam'iyyar mai riya kare hakkin nbila'adama ta National Democratic Front wacce take da rinjaye a majalisar dokokin kasar ta Myanmar. A lokacin da har'ila yau Ansansuchi shugaban Jam'iyyar tana matsayin Ministan harkokin wajen kasar kuma tana da fada a ji a cikin gwamnatin Kasar.

Wani abin lura da Malam Ansansuchi shi ne ta karbi kyautar Nobel na zaman lafiya don irin gwagwarmayan da ta yi na samarwa mutanen kasarta Nyemcin zabin shuwagabannin da suke so da kuma 'yencin walwala a cikin kasar. Shirun da Malam Ansansuchi ta yi a kan wahalhalun da musulman kasar Rohinga suke ciki wani aibi ne a matsayinta wacce ta shahara kuma har ta karbi kyautar Nobel kan kare hakkin mutanen kasar sa. 

Wasu masana suna ganin shirin da malama susanchi ta yi yana daga cikin abinda ya karfafawa jami'an tsaro da kuma masu tsattsaurarra ra'ayin kisan addin Buza fadawa musulman kasar kasar Myanmar.

Banda haka a lokacinda malama Sunsan chin ta je birnin Toyo na kasar Japan a makonnin da suka gabata yan jarada sun yi mata tambaya kan yadda tashe tashen hankula suke tashi a yankin na rahin sai ta bayana cewa gwamnatin kasar zata dauki matakan da suka dace don ladabtar da jami'an tsaronn kasar wadanda suke da hannu wajen kashe al-ummar musulman kasar Tsiraru. Sai dai har yanzun makonni fiye da biyu da wannan jawabin amma ba tare da wani abu ya chaza a cikin halin da musulman kasar ta Myanmar suke ciki ba.