Bukatar Banki Moon na girmama 'yan gudun hijra
https://parstoday.ir/ha/news/world-i14044-bukatar_banki_moon_na_girmama_'yan_gudun_hijra
Babban Saktaren MDD ya bukaci kungiyoyin kasa da Kasa na Duniya da su karfafa hakuri da juriya a zaman tare da girmama 'yan gudun hijra da bakin haure a Duniya
(last modified 2018-08-22T06:59:15+00:00 )
Nov 17, 2016 14:43 UTC
  • Bukatar Banki Moon na girmama 'yan gudun hijra

Babban Saktaren MDD ya bukaci kungiyoyin kasa da Kasa na Duniya da su karfafa hakuri da juriya a zaman tare da girmama 'yan gudun hijra da bakin haure a Duniya

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa daga Birnin New York  ya nakalto saktare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon cikin wani jawabi da ya gabatar jiya Laraba dangane da ranar karfafa hakuri da juriya a zaman tare na MDD na cewa kyakkyawar mu'amala tare da karfafa hakuri da juriya a zaman tare na daga cikin mahiman batutuwan da suka gina Majalisar Dinkin Duniya.

Banki Moon ya ce 'yan gudun hijra da Bakin haure suma na jurewa kadaita na zama a wata kasa da ba kasar su ba domin haka kyakkyawar mu'amala tare da su shi ne zai sassauta musu irin zafin kadaicin da kuncin da suke fuskanta na zama a wata kasar da ba ta su ba.

Har ila yau Banki Moon ya bukaci Al'ummar Duniya da su yi  kokari wajen karfafa hakuri da juriya a zaman tare, wanda hakan shi zai sanya a samu Duniya guda 'yantatta.

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe duk ranar 16 ga Nuwamban kowace shekara, domin karfafa hakuri da juriya a zaman tare. An fara bikin ranar ne a shekarar 1995 da nufin wayar da kan jama’a a kan rashin hakuri da juna a zamantakewa, shekarar ta bana dai an bata taken (mu dukka tare) da nufin rage mumunar kallon da Al'umma ke yiwa 'yan gudun hijra da Bakin haure a Duniya.