Ci Gaba Da Sayen Makaman Amurka Da Kasashen Larabawa Suke Yi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i14176-ci_gaba_da_sayen_makaman_amurka_da_kasashen_larabawa_suke_yi
A kwanakin baya ne kasar Kuwait ta sanar da kulla wata yarjejeniya ta sayen makamai daga wajen Amurka don abin da ta kira karfafa irin karfin sojin da take da shi, inda ta ce za ta sayo jiragen yaki na zamani samfurin F18 da kudinsu ya kai Dala biliyan 10 wanda hakan ne ita ce mafi girman yarjejeniyar sayen makami da kasar Kuwaitin da taba kullawa tsawon tarihinta.
(last modified 2018-08-22T06:59:16+00:00 )
Nov 21, 2016 01:59 UTC
  • Ci Gaba Da Sayen Makaman Amurka Da Kasashen Larabawa Suke Yi

A kwanakin baya ne kasar Kuwait ta sanar da kulla wata yarjejeniya ta sayen makamai daga wajen Amurka don abin da ta kira karfafa irin karfin sojin da take da shi, inda ta ce za ta sayo jiragen yaki na zamani samfurin F18 da kudinsu ya kai Dala biliyan 10 wanda hakan ne ita ce mafi girman yarjejeniyar sayen makami da kasar Kuwaitin da taba kullawa tsawon tarihinta.

Kafin wannan lokacin dai kasar Kuwaitin ba ta taba kulla wata yarjejeniya ta sayen makamai irin haka ba, to amma cikin shekara gudan da ta gabata, duk kuwa da matsalar faruwar farashin man fetur a kasuwar duniya, sai ga shi kasar Kuwaitin ta fada wannan fage na sayen makamai.

Cikin 'yan shekarun baya-bayan nan dai kasashen larabawan Tekun Fasha, musamman kasar Saudiyya, sun zamanto su ne kan gaba cikin kasashen duniya wajen sayen makaman kasar Amurka. Ta yadda cikin wadannan shekarun kasar Amurkan ta sayar wa wasu kasashen larabawan Tekun Fashan da makaman da kudadensu ya kai Dala biliyan 33.

A zahiri dai kasashen larabawan Tekun Fasha sun sanar da cewa tabbatar da tsaronsu shi ne dalilin da ya sanya su gayyata da kuma daukan bakuncin sojojin Amurka a kasashen na su, to sai dai daga dukkan alamu Amurka ita ce mai gagarumar amfanuwa da wannan kasantuwa na ta a kasashen larabawan Tekun Fasha kafin ma a je ga wani batu na tabbatar da tsaro da zaman lafiyan wadannan kasashen.

Don kuwa daya daga cikin manyan hanyoyin da Amurka take samun kudaden shigarta ita ce hanyar sayar da makamai ga kasashen duniya musamman kasashen larabawan Tekun Fasha. A shekara ta 2014 ta kasance ita ce kasar da ke kan gaba wajen sayar da makamai sakamakon sayar da makaman da kudadensu suka kai dala biliyan 24, wanda hakan yana a matsayin kashi daya cikin uku na dukkanin makaman da aka sayar a duniya. Cikin wadannan dala biliyan 24 kuwa, dala biliyan 9 sun fito ne daga kasashen Yammacin Asiya musamman kasashen larabawan Tekun Fashan.

Fitar da wadannan rahotanni na irin makudan kudaden da kasashen larabawan Tekun Fasha suke warewa don sayen makamai suna zuwa ne a daidai lokacin da cibiyoyin kuli na kasa da kasa irin cu Bankin Duniya da kuma Asusun Lamuni na Duniyan (IMF) cikin rahotannin da suka fitar a baya-bayan nan suna ni da irin matsalar tattalin arziki da wadannan kasashe na Tekun Fasha suke fuskanta sakamakon faduwar farashin man fetur da suka dogara da su. Bisa wadannan rahotanni shida daga cikin kasashen larabawan Tekun Fashan da suka hada da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Oman, Kuwait da Bahrain suna fuskantar matsanancin karayar tattalin arziki da ba su taba ganin irin sa ba wanda hakan zai iya sanya su cikin matsaloli daban-daban cikinsu kuwa har da matsala ta zamantakewa.

Irin wannan rigegeniya wajen sayen makamai da kasashen Tekun Fashan suke yi tana zuwa ne a daidai lokacin da wani bangare na wadannan makamai suna ba da su ne ga kungiyoyin 'yan ta'addan da suke yankin musamman na kasashen Iraki da Siriya.

A irin wannan yanayin ne wasu manazarta harkokin siyasa suke ganin irin sayen makaman da wadannan kasashen suke yi ba tare da lissafi ba wani kokari ne kawai na tseratar da kasashen yammaci musamman Amurka daga matsalar tattalin arzikin da take fuskanta da kuma hana kamfanoni masu kera makaman rugujewa. Kamar yadda wasu kuma suke ganin irin rikice-rikicen da kasashen Yammacin musamman Amurka suke kirkiro su a yankin Gabas ta tsakiyan suna da alaka da samun damar sayar da makaman da suke yi da kuma dawo da dalolin da suke ba wa larabawan wajen sayen man fetur dinsu.