Putin ya bayana cewa aiki da Obama nada wahala
Shugaban Kasar Rasha ya ce a yayin milkin Obama Masco ta yi ta kokari wajen dawo da alakar kasashen biyu kamar yadda yake a baya to saidai aiki da Obama na da matsanacin wahala
A yayin da yake gabatar da jawabi gaban manema labarai a karshen taron kungiyar APEC da ya gudana jiya lahadi a birnin Lima na kasar Peru ya ce zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi masa alkawari a lokacin shugabancin sa Watsinton za ta gyara alakar ta da birnin Masco.
A bangare guda Shugaban kasar Rashan Viladimin Putun ya gana da Shugaban kasar Amurka mai barin gado Barak Obama a gefen taron kungiyar tattalin kasashen yankin Asia da Pacific watau APEC , inda suka tattauna kan rikicin kasashen Siriya da Ukreine.
Alaka tsakanin kasashen Amurka da Rasha ta fuskanci koma baya tun a shekarar 2014 bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta kusa kan iyakar kasar ta Rasha daga gabashin kasashen Turai musaman ma Sojojin Amurka da kuma sabani dake tsakanin kasashen biyu dangane da rikicin kasar Siriya.