Cuba: Duniya Na ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Fidel Castro.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i14431-cuba_duniya_na_ci_gaba_da_alhinin_mutuwar_fidel_castro.
An Zaman Makoki A Kasar Cuba Na mutuwar Castro
(last modified 2018-08-22T06:59:18+00:00 )
Nov 26, 2016 15:23 UTC
  • Cuba: Duniya Na ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Fidel Castro.

An Zaman Makoki A Kasar Cuba Na mutuwar Castro

Tashar Telbijin din gwamnatin kasar Cuba, ta sanar da cewa za a yi zaman makoki na tsawon kwanaki 9 saboda mutuwar tsohon shugaban kasar Fidel Castro.

A  cikin kasar ta Cuba, an yi kasa da tutar kasar a cikin dukkanin gine-gine gwamnati da kuma cibiyoyin soja.

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike da sakon ta'aziyyar mutuwar Fidel Castro ga shugaban kasar na yanzu, Raol Castro da a cikin ya bayyana alhininsa.

Shugaba Rauhani ya ce;  Da akwai wasu naui na mutane wadanda su ke yin gwagwarmaya da zalunci da take hakkin bil'adama da ya zama ruwan dare, ba kuma za su yi sassauci ba har mutuwarsu.

Shugaban kasar ta Iran, ya bayyana Fidel Castro da cewa; Dan juyin juya hali ne wanda baya gajiya ko yin rauni.

Shugaban kasar Blovia, Evo Morales ya ce; samar da hadin kai a tsakanin al'ummun duniya shi ne tunawa mafi muhimmanci da za a yi wa Castro.

Shugaban kasar Fransa, Fransua Hollande ya bayyana Castro a matsayin fitaccen mutum da ya rayu a karni na ashrin.

 Shi kuma shugaban kasar Rasha, vlademir Putin ya ce; Fidel Castro ya zama wani alami na wannan zamanin.

Da safiyar yau asabar ne dai kafafen watsa labarun kasar ta Cuba su ka sanar da mutuwar fidel Castro wanda ya jagoranci juyin juya halin kasar har zuwa nasara a 1959.