An kawo karshen zaman kwararru na kungiyar OPEC
A safiyar jiya Litinin kwararu na Kungiyar OPEC daga kasashen 14 sun gudanar da zama na a'o'i goma sha daya a cibiyar kungiyar dake birnin Vienna.
Bayan kammala wannan zama, kwararrun sun gabatar da wasu shawarwari da zai taimakawa kungiyar wajen farfado da farashin Man fetur a Duniya, kuma wadannan shawarwari sun gabatar da su ga Ministocin kungiyar domin ya samu amincewa.
Yayin da suke barin saktariyar Kungiyar ta OPEC a daren jiya Litinin, kwararun sun ki cewa komai dangane da shawarwarin da suka gabatar.
A gobe labara ce kungiyar ta OPEC za ta bude taron ta karo na 171 a cibiyar ta dake birnin Vienna, kuma ana sa ran taron zai tattauna tare da daukan mahiman matakai kan yarjejjeniyar da Ministocin kungiyar suka cimma wa na rage yawan Man fetur din da suke hakowa ko wata rana a birnin Alje na kasar Aljeriya.