Ana Barazanar Kona Masallaci A Michigan Amurka
A cikin wata wasika da aka aike zuwa ga babban masallacin Michigan a kasar Amurka an yi barazanar yin kisan kiyashi a mulkin Donald Trump kan masallata irin na Hitler.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na «clickondetroit» cewa, Dawud Khalid shugaban cibiyar musulmi reshen jahar Michigan ya bayyana cewa, a cikin wasikar da aka aike ga masallacin an bayyana cewa, Donald Trump zai kona musulmi kamar yadda Hitler ya kona yahudawa.
Baya ga barazana a kan rayuwar musulmi da ke cikin wasikar, haka nan kuma tana dauke d kalaman batunci a kan musulmi da addinin muslunci, tare da bayyana cewa wannan shi ne mataki mafi dacewa a Amurka.
Khalid ya kara da cewa, wannan shi ne karon farko da aka samu irin wannan wasika da aka rubuta zuwa ga wannan masallaci, duk kuwa da cewa an yi irin hakan ga wasu masallatai a cikin jahohin Indiana da California gami da Georgia.
Ya kara da cewa ba su da wani zabi illa su su dauki matakan kare kansu, da kuma bin hanyoyi na doka domin tabbatar da cewa an kare hakkokinsu kamar sauran ‘yan kasa.