Al'ummar kasar Cuba sun yi ban kwana da Fidel Castro
Cikin wani yanayi na jimami da alhini shugaban kasar Cuba Raul Castro ya yi alkawarin ci gaba da akidar dan uwansa Fidel Castro.
Shugaban kasar Cuba Raul Castro ya sha alwashin ci gaba da akidar gwagwarmayar juyin juya hali na dan uwansa Fidel Castro a wani gagarumin gangami da aka yi na karrama marigayin kafin a binne tokar gawarsa.
Dubban jama'a sun hallara dauke da tutoci su na rera wakokin gwagwarmyar juyin juya hali da ke tunatarwa da gudunmawar da marigayi Fidel Castro ya bayar wajen cigaban kasar.
Mutuwar fidel Castro ta haifar da zulumi akan ko wane tafarki kasar za ta dauka bayan rashin mutumin da ya jagoranci kasar kusan shekaru hamsin. Jama'a cikin alhini suna zubar da hawaye na tunanin yadda Castro ya bayar da Ilmi kyauta da kuma inganta tsarin lafiya a kasar.