Amnesty Int. : Kisan Musulmin Rohingya A Myanmar Laifukan Yaki Ne
https://parstoday.ir/ha/news/world-i15463-amnesty_int._kisan_musulmin_rohingya_a_myanmar_laifukan_yaki_ne
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty Int. ta soki lamirin gwamnatin kasar Myanmar dangane da kisan musulmi 'yan kabilar Rohingya, tare da bayyana hakan a matsayin laifin yaki da kotun duniya za ta iya daukar mataki a kansa.
(last modified 2018-08-22T06:59:25+00:00 )
Dec 19, 2016 07:19 UTC
  • Amnesty Int. : Kisan Musulmin Rohingya A Myanmar Laifukan Yaki Ne

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty Int. ta soki lamirin gwamnatin kasar Myanmar dangane da kisan musulmi 'yan kabilar Rohingya, tare da bayyana hakan a matsayin laifin yaki da kotun duniya za ta iya daukar mataki a kansa.

Tashar Press TV ta bayar da rahoton cewa, a cikin baynin wanda kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty Int. ta fitar a jiya, ta bayyana cewa dole ne gwamnatin Myanmar ta dakatar da kisan ta take yi wa musulmi 'yan kabilar Rohingaya, kuma dole ne a kafa wani kwamitin bincike na kasa da kasa wanda zai gudanar da bincike na gaskiya da adalci, dangane da kisan da sojojin gwamnatin mayanmar suka yi wa musulmin Rohingya.

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne dai sojojin gwamnatin Myanmar suka kaddamar da hare-hare a kan yankunan da 'yan kabilar Rohinya suke zama, inda suka kashe daruruwa daga cikinsu, da kuma jikkata wasu dubbai ,tare da korar sama da dubu 30 daga muhallansu.