Bukatar MDD na taimakawa Al'ummar Palastinu.
MDD ta bukaci Kungiyoyin kasa da kasa da su taimakawa Al'ummar Palastinu da tsabar kudi sama da miliyan 500$ a shekarar 2017
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Robert Piper jami'in huldar kungiyar Agaji ta MDD a yankin Palstinu na cewa kimanin Mutane miliyan daya da dubu dari na yankin Zirin Gaza da kuma Mutane dubu dari biya na yankin kogin Jodan ke bukatar taimakon gaggawa na tsabar kudu kimanin miliyan 547 na $.
Wannan shelar neman taimako na zuwa ne a yayin da shekarar 2016 ke karewa, inda a cikin ta taimakon dala miliyan 267 ne kawai aka samu daga cikin miliyan 570 da MDD ta bukata aka samu domin taimakawa Al'ummar Palastinun.
Mista Piper ya kara da cewa bayan wannan taimako wajibi ne kungiyoyin kasa da kasa su kara kokari wajen ganin an samu maslaha tsakanin Al'ummar Palastinu da kuma Mahukuntar haramcecciyar kasar Isra'ila da zai sanya Al'ummar Palastinun su samu sa'ida a rayuwansu.