Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Yana Ziyarar Aiki A Bonina Faso
https://parstoday.ir/ha/news/world-i1603-babban_sakataren_majalisar_dinkin_duniya_yana_ziyarar_aiki_a_bonina_faso
Babban sakataren Majalisar dinkin suniya Banki Moon ya fara wani ziyarar aiki a
(last modified 2018-08-22T06:57:53+00:00 )
Mar 03, 2016 06:59 UTC
  • Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Yana Ziyarar Aiki A Bonina Faso

Babban sakataren Majalisar dinkin suniya Banki Moon ya fara wani ziyarar aiki a

Babban sakataren Majalisar dinkin suniya Banki Moon ya fara wani ziyarar aiki a kasar Borkina Faso. Shafin yanar gizo na Afrika Time ya ce babban sakataren ya isa birnin wagadugu a jiya Laraba inda ministan harkokin waje na kasar Alpha Barry ya tarbe shi. Kuma ana saran a yau Alhamis ne babban sakataren zai gana da shugaba Roch Marc Christian Kaboré sannan ya ziyarci wata cibita ta kule da renon yara kanana wadanda suke fama da cutar HIV/AIDS.

Kafin haka dai babban sakataren ya yabawa mutanen kasar Borkina Faso kan gudanar da zabubbuka na shugaban kasa da Majalisar dokoki cikin lumani da zaman lafiya.

Daga kasar Borkina Faso ana saran babban sakataren zai ziyarci wasu kasashen Afrika biyu, wadanda suka hada da Mauritania da kuma Algeria.