Kiferwar Kwale-kwalen 'Yan gudun Hijira A Tekun Midetreniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16609-kiferwar_kwale_kwalen_'yan_gudun_hijira_a_tekun_midetreniya
Wani kwale-kwale mai dauke da'yan ci-rani 107 ya yi kuli-kulin kubura a cikin tekun midetreniya.
(last modified 2018-08-22T06:59:32+00:00 )
Jan 15, 2017 04:01 UTC
  • Kiferwar Kwale-kwalen 'Yan gudun Hijira A Tekun Midetreniya

Wani kwale-kwale mai dauke da'yan ci-rani 107 ya yi kuli-kulin kubura a cikin tekun midetreniya.

Wani kwale-kwale mai dauke da'yan ci-rani 107  ya yi kuli-kulin kubura a cikin tekun midetreniya a jiya asabar.

Kamfanin dillancin labarun "Ansa" ya ambaci cewa; A jiya asabar ne masu aikin ceto na kasar Italiya su ka yi nasarar ceto da mutane uku kadai daga cikin 107 da su ke cikin kwale-kwalen, da su ma yanayin lafiyarsu ya tabarbare. An kuma dauke su a wani jirgi mai saukar angulu zuwa asibiti a cikin kasa ta Italiya.

Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan makomar sauran 'yan ci ranin da su ka nutse.

A shekaran jiya juma'a ma dai masu aikin ceton na kasar Italiya sun yi nasarar tsaratar da wasu 'yan ci rani 550 a tsibirin Lampe Doza.

Shekarar 2016 da ta gabata an sami 'yan ci rani 181,000 da su ka shiga kasar Italiya. Wannan shi ne adadi mafi yawa na 'yan gudun hijira da su ka shigar kasar fiye da shekarar 2015 da kaso 18%.