Iran Ta Bukaci Gwamnatin Myanmar Ta Kawo Karshen Kissan Musulman Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16813-iran_ta_bukaci_gwamnatin_myanmar_ta_kawo_karshen_kissan_musulman_kasar
gwamnatin kasar Iran ta bukaci gwamnatin kasar Myanmar da ta kawo karshen kisan kiyashin da akewa muslman kabilar Rohinga
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 19, 2017 08:16 UTC
  • Iran Ta Bukaci Gwamnatin Myanmar Ta Kawo Karshen Kissan Musulman Kasar

gwamnatin kasar Iran ta bukaci gwamnatin kasar Myanmar da ta kawo karshen kisan kiyashin da akewa muslman kabilar Rohinga

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi yana fadar haka a yau Alhamis a taron gaggawa wanda kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta kira a birnin Kwalalanpa na kasar Malasia.

Abbas Araqchi ya kara da cewa ba zai yi halin da musulman kabilar Rokhinga suke ciki a kasar Myanmar ya ci gaba ba, dole ne gwamnatin kasar ta nemi hanyar kawo karshen wahalhalun da musulman kabilan rohinga suke ciki a kasar.

A yau Alhamis ne kungiyar ta OIC ta fara taron gaggawa don tattauna batun na musulman kasar Myanmar da kuma wasu matsalolin kasashen wadanda suka hada da yaki da ayyukan ta'addanci.

Kasashen kungiyar ta OIC 57 zasu dubi hanyoyin kawo karshen wahalar da musulman kasar ta Myanmar suke ciki wanda tun somawarsa yayi sanadiyyar mutuwar mutane 500 sannan da kona gidaje masallatai makarantu da kuma kona wasu kauyuka guda ukku.