An Rantsar Da Trump A Matsayin Shugaban Amurka Na 45
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16876-an_rantsar_da_trump_a_matsayin_shugaban_amurka_na_45
Zababen shugaban Amurka Donald Trump, ya yi rantsuwar kama aiki a matsayinsa na shugaban kasar na 45, inda ya gaji Barack Obama wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 8.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jan 20, 2017 14:15 UTC
  • Donal Trump, ya zama shugaban Amurka na 45.
    Donal Trump, ya zama shugaban Amurka na 45.

Zababen shugaban Amurka Donald Trump, ya yi rantsuwar kama aiki a matsayinsa na shugaban kasar na 45, inda ya gaji Barack Obama wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 8.

Babban jojin Amurka ne John Roberts, ya rantsar da Mista Trump a bikin da akayi yau Juma'a a birnin Washigton.

Bayan rantsarda dashi, a cikin jawabinsa Mista Trump ya ce "lokacin fada ba cikawa ya wuce, yanzu lokacin aikatawa ne''

Hakazalika a cikin jawabin na sa na farko a matsayin shugaban Amurka, Trump ya ce ''Ba zan kara amincewa da 'yan siyasa masu fada ba cikawa ba''

Saida alkalin kotun kolin Amurka, Clarence Thomas ya rantsar da Mike Pence a matsayin mataimakin shugaban Amurka, kafin daga bisani a rantsarda Mista Trump.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin hada tsohon shugaba Obama da matarsa Michel, sai kuma 'yar takara demokrate data sha kayi a zaben Hillary Cliton da mai gidanta tsohon shugaba Bill Cliton da kuma tsohon shugaba George W Bush.