Kasar Mexico ba za ta biya kudaden gina Katanga ba
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17033-kasar_mexico_ba_za_ta_biya_kudaden_gina_katanga_ba
Shugaban kasar Amurka ya ce idan Kasar Maxico ta ki amincewa da biyan kudaden gida katanga a kan iyakokin kasashen to ba zai gana da Shugaban kasar Maxicon ba.
(last modified 2018-08-22T06:59:35+00:00 )
Jan 26, 2017 14:09 UTC
  • Kasar Mexico ba za ta biya kudaden gina Katanga ba

Shugaban kasar Amurka ya ce idan Kasar Maxico ta ki amincewa da biyan kudaden gida katanga a kan iyakokin kasashen to ba zai gana da Shugaban kasar Maxicon ba.

Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto Shugaban kasar Amurka Donald Trump a wannan Alkhamis na cewa matukar magabatan kasar Maxico suka ki amincewa da biyan kudaden gina katanga a kan iyakar kasar da Amurka to wajibi shugaba Enrique Pena Nieto na Maxico ya dage ziyarar da yake son kawowa a makun gobe domin kuwa ba zan gana da shi ba.

Shugaba Trump wanda ya dare kan karagar milki a kasa da maku guda, a daren jiya Laraba ya bayar da umarnin gina katanga tsakanin iyakar kasar sa da kasar Maxico,matakin da ya harzuka sauran shugabannin Yankin.

A matsayin mayar da martani,Shugaban Kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya yi allawadai da shirin shugaban Amurka Donald Trump na gina Katanga tsakanin kasashen biyu kamar yadda ya bayar da umurni.

A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar, shugaba Nieto ya ce Mexico na bukatar a mutuntata a matsayin kasa mai ‘yanci. sannan kuma ya ce kasar ba za ta biya sisin kwabo ba ga aikin gina katangar da Trump ya ce ita za ta biya.