Amurka : Trump, Zai Tattauna Da Shugabannin Kasashe 5 Ta Wayar Tarho
Sabon shugaban Amurka, Donald Trump zai tattauna ta wayar tarho da wasu shugabannin kasashen waje biyar a wannan Asabar.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce Mista Trump zai tattauna da shugaba Vladimir Poutine na Rasha da firaministan Japan Shinzo Abe, da na Austrea Malcolm Turnbull, sai kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma shugaba François Hollande na Faransa.
Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaba Trump ya gana da firaministar Britaniya Theresa May jiya Juma'a a fadar White House.
Mista Trump dai ya yabi matakin da Britaniya ta dauka na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai inda ya ce matakin zai bai wa kasar zabi kan karbar baki da gudanar da hada-hadar kasuwanci.
Theresa May ce shugabar da ta soma kai ziyara a Amurka tun bayan da aka rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka a makon da ya gabata.