Rasha ta gargadi Amurka kan sanyawa Iran sabon takunkumi
Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta gargadi kasar Amurka da kawo cikas kan yarjejjeniyar da manyan kasashe biyar gami da kasar Jamus suka cimma na makamashin Nikiliyar Iran na zaman Lafiya
A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alkhamis Ma'aikatar Harakokin wajen Rasha ta bukaci Amurka da ta kuji sake kakabawa Jumhoriyar musulinci ta Iran wani sabon takunkumi da hakan zai iya janyo illa ga yarjejjeniyar da manyan kasashe biyar masu kujerar dindin din a MDD gami da kasar Jamus suka cimma tare da kasar Iran dangane da shirinta na Nikiliyar zaman Lafiya.
Ma'aikatar ta bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani kan Labarin cewa a kwai yiyuwar Washinton ta sake kakabawa Jamhoriyar musulinci ta Iran wani sabon takunkumi.
A nata Bangare, Kungiyar tarayyar Turai ta bukaci Amurka da ta mutunta yarjejjeniyar da aka cimma da kasar Iran kuma ta guji aiwatar da duk wani abu da zai kawo illa ga yarjejjeniyar.
A baya dai, Sabon Shugaban kasar ta Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai keta yarjejjeniyar da aka cimma da kasar Iran game da shirin Nukiliyar ta na zaman Lafiya, a yayin da magabatan kasar ta Iran ke ci gaba da bayyana cewa za su ci gaba da mutunta wannan yarjejjeniya matukar dai bangaren kasashen Turai da Amurkan suka ci gaba da mutunta ta.