Ya Kamata Gwamnatin Japan Ta Tsawata Kan Matakin Trump
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17291-ya_kamata_gwamnatin_japan_ta_tsawata_kan_matakin_trump
Jagorar 'yan adawa a kasar Japan, Renho ta bukaci firaministan kasar Shinzo Abe daya tsoma baki kan matakin hana 'yan gudun hijira shiga AMurka na shugaba Donald Trump.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 03, 2017 02:10 UTC
  • Ya Kamata Gwamnatin Japan Ta Tsawata Kan Matakin Trump

Jagorar 'yan adawa a kasar Japan, Renho ta bukaci firaministan kasar Shinzo Abe daya tsoma baki kan matakin hana 'yan gudun hijira shiga AMurka na shugaba Donald Trump.

Wadanan kalaman na Mme Renho na zuwa ne kwanaki kadan kafin babban taron Amurka da Japon.

Shi dai firaministan Japon Shizo Abe ya bayyana a jiya Alhamis cewa ba zaiyi magana ba dangane da matakin na Trump, saboda a cewarsa batun 'yan gudun hijira da kuma dokokinsa batu ne na siyasa cikin gida. 

Saidai a cewar jagorar 'yan adawa ta Japon ta ce hakkin AMurka da Japon su kare 'yancin bil adama, don haka tana son firaministan kasar ya farka daga kwana ya tsawata ya fadi abunda ya kamata a fada kan wannan matakin na Trump.

Shi dai matakin sabon shugaban na Amurka Donald Trump wanda ya tanadi hana baki da daga wasu kasashen musulmi bakwai da kuma 'yan gudun hijira shiga Amurka ya tayarda zazzafar muhawara da kuma tofin alla-tsine daga shugabannin kasashen duniya da dama.

Japon dai iata ce kasa kawar Amurka a jerin kasashen mafi arziki a Duniya na G7 da bata ce uffan ba dangane da matakin na Trump.