Ma'aikatar Shari'a Amurka Ta Daukaka Kara Kan Watsi Da Matakin Trump
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17345-ma'aikatar_shari'a_amurka_ta_daukaka_kara_kan_watsi_da_matakin_trump
Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta daukaka kara kan hukuncin da wata kotun kasar ta yanke na yin watsi da matakin hana baki daga kasashe bakwai na musulmi shiga Amurka na Shugaba Donald Trump.
(last modified 2018-08-22T06:59:38+00:00 )
Feb 05, 2017 07:16 UTC
  • Ma'aikatar Shari'a Amurka Ta Daukaka Kara Kan Watsi Da Matakin Trump

Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta daukaka kara kan hukuncin da wata kotun kasar ta yanke na yin watsi da matakin hana baki daga kasashe bakwai na musulmi shiga Amurka na Shugaba Donald Trump.

Trump, ya fada a shafinsa na Tweeter cewa watsi da matakinsa wauta ne kana zai baiwa mutane masu muguwar anniya da masu hadari sosai shiga kasar ta Amurka.

A ranar juma'a data gabata ne dai alkali James Robert, da ke yankin Sattel a jahar Washington ya yanke hukuncin jingine aiki da dokar ta Trump har sai an duba batun koken dake gaban babban mai sharia na Washington.

Matakin Trump din dai ya janyo zanga-zangar dubban mutane daga biranen London da New York da Washington.