Amurka Ta Kashe Wani Babban Kwamandan Al'Qaida A Syria
Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da hallaka Abou Hani al-Masri, wani babban kwamandan kungiyar Al'Qaida a wani harin sama data kai a kasar Syria.
An dai hallaka Al-Masri ne a yankin Idleb a ranar 4 ga watan Fabrairu nan kamar yadda kakakin ma'aikatar ta Pentagone, Jeff Davis ya sanar.
An dai bayyana Al-Masri a matsayin mai alaka da Usama Ben Laden da kuma jagoran kungiyar Al'Qida na yanzu Ayman al-Zawahiri.
Hakazalika a cewar sanarwar Al-Masri ya jagoranci kafa rassan kungiyar da dama a Afganistan a cikin shekara 1980 da 1990, inda ya horada tare da daukan dubban 'yan ta'adda da suka yadu a duniya.
Hare haren da AMurka ke kaiwa a Syria sun dai fi shafar 'yan ta'addan IS, saidai a baya bayan nan ta zazafa kai hare haren kan 'yan ta'addan Al'Qaida.