Trump Ya Nada Sabon Mashawarci Kan Harkokin Tsaro
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17858-trump_ya_nada_sabon_mashawarci_kan_harkokin_tsaro
Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar da nada Janar Herbert McMaster, a matsayin mai bashi shawara kan harkokin tsaron kasa, inda zai maye gurbin Michael Flynn wanda ya yi murabus a makon da ya gabata.
(last modified 2018-08-22T06:59:42+00:00 )
Feb 21, 2017 02:23 UTC
  • Trump Ya Nada Sabon Mashawarci Kan Harkokin Tsaro

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar da nada Janar Herbert McMaster, a matsayin mai bashi shawara kan harkokin tsaron kasa, inda zai maye gurbin Michael Flynn wanda ya yi murabus a makon da ya gabata.

Mr.Trump ya ce Janar McMaster, mutum ne mai basira da kuma fasaha ta gudanar da wannan aiki, kuma ana mutunta shi a rundunar sojan kasar.

A nasa bangare kuma, Janar McMaster dan shekaru 54 ya bayyana cewa, zai dukufa wajen kiyayewa, da kuma kyautata yanayin tsaron Amurkawa.

A ranar 13 ga wata ne mai baiwa shugaban na Amurka shawara kan harkokin tsaron kasa Michael Flynn ya yi murabus, sabo da samun shi da laifin tattaunawa ta wayar tarho da jakadan kasar Rasha dake Washington, alhali tsohon shugaban kasar Barack Obama na kan karagar mulki, lamarin da ya sa, ya kasance babban jami'i na farko da ya yi murabus bayan Donald Trump ya dare karagar mulkin kasar ta Amurka.