Sabbin matakan koran bakin haure a kasar Amurka.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17918-sabbin_matakan_koran_bakin_haure_a_kasar_amurka.
Ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka ta sanar da sabbin matakai da take shirin dauka domin gaggawar kwashe milyoyin baki da ke zaune a kasar ba tare da mallakar takardun izinin zama ba.
(last modified 2018-08-22T06:59:43+00:00 )
Feb 22, 2017 07:30 UTC
  • Sabbin matakan koran bakin haure a kasar Amurka.

Ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka ta sanar da sabbin matakai da take shirin dauka domin gaggawar kwashe milyoyin baki da ke zaune a kasar ba tare da mallakar takardun izinin zama ba.

Bincike ya nuna cewa sama da mutane miliyan 11 ne aka tabbatar da cewa suna zaune a Amurka, ba tare da mallakar takardun izinin zama ba, kuma sabbin matakan da za’a dauka za su shafe su matukar aka aiwatar da su.

A matakin farko sakataren tsaron cikin gida John Kelly, ya bai wa jami’an shige da fice da kuma hukumar kwastam izinin gaggauta tasa keyar marasa takardu da ke zaune a kasar.

An karkasa bakin hauren zuwa gida 7, na farko da za’a kwashe, su ne wadanda aka samu da aikata laifuka a Amurka, da wadanda ake zargi da aikata laifukan, kafin kotu ta tabbatar da hakan.

Haka zalika matakin zai rusa wata doka da tsohon shugaban kasar Barack Obama ya dauka a shekara ta 2012, wadda ke bai wa marasa takardu damar zama a kasar ta Amurka.