Za'a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Equador
Majalisar zabe a Equador, ta ce za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar, bayan da aka kasa samun wanda ya samu adadin kuri'un da ake bukata domin lashe zaben tun zagayen farko.
A ranar Lahadi data gabata ne al'ummar Equador suka kada kuri'a domin zaben shugaban kasa, tsakanin dan takara gurguzu Lenin Moreno da kuma tsohon ma'aikacin banki Guillermo Lasso.
Za'a dai je zagaye na biyu ne a ranar 2 ga watan Afrilu na wannan shekara kamar yadda shugaban majalisar zabe ta kasar (CNE), Juan Pablo Pozo ya sanar a cikin daren jiya Laraba a gidan talabijin da radio na kasar ta Equador.
Mista Pozo, ya ce sakamakon kidayar kuri'un zaben daya samu fitowar jama'a da kashi 99%, babu dan takara daya samu rinjayen da ake bukata na kashi 40% don yin nasara tun zagayen farko.
Sakamakon zaben dai ya nuna dan takara Lenin Moreno, wanda na hannun daman tsohon shugaban kasar ne Rafael Correa, a sahun gaba da kashi 39,3 yayin da abokin hamayyarsa Guillermo Lasso, mai ra'ayin rikau ke da kashi 28,1% na yawan kuri'un da aka kada.