Ministan Harkokin Wajen Faransa: Babu Alaka Tsakanin Ta'addanci Da Muslunci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18134-ministan_harkokin_wajen_faransa_babu_alaka_tsakanin_ta'addanci_da_muslunci
Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana cewa, babu wata alaka a tsakanin addinin musulunci da ta'addanci.
(last modified 2018-08-22T06:59:45+00:00 )
Mar 01, 2017 15:20 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Faransa: Babu Alaka Tsakanin Ta'addanci Da Muslunci

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana cewa, babu wata alaka a tsakanin addinin musulunci da ta'addanci.

Jaridar Jakarta Club ta bayar da rahoton cewa, a ziyarar da ministan harkokin wajen kasar ta Faransa yake gudanarwa  a kasar Indonesia, kasar  musulmi wadda tafi sauran kasashen msuulmi yawan jama'a, ya bayyana cewa ayyukan ta'addanci daban addinin muslunci daban.

Dangane da irin yadda ake takura musulmi a kasashen turai da nuna musu kyaa kuwa, ministan na Faransa ya bayayna cewa kasar Faransa tana kallon 'yan kasarta a matsayin al'umma guda, ba tare da nuna wani banbanci a tsakanin addinai, domin a cewarsa kowane mutum yana da hakkin ya bi addinin da yake so ko akidar da ya ga dama.

Ya bayyana ayyukan ta'addanci a matsayin abin da ke barazana ga daukacin kasashen turai, da na asia da kuma yankin gabas ta tsakiya.