Jawabin Shugaban Amurka Trump A Gaban 'Yan Majalisun Tarayyar Kasar
A jawabinsa na farko a gaban 'yan majalisun tarayyar Amurka, shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada irin rauni da tsaka mai wuyar da Amurkan take ciki, yana mai shan alwashin sake dawo wa Amurkan da 'mutumci da kuma daukakar' da take da ita.
A cikin wannan jawabi da ya gabatar a jiya Laraba, shugaba Trump ya bayyana cewar abin da a halin yanzu yake kokarin yi shi ne gagarumin kokari na dawo da mutumcin Amurkan wanda nan ba da jimawa ba kawayen Amurkan za su fahimci cewa Amurkan ta sake dawowa da shirinta na jagoranci.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin mummunan yanayin da Amurkan take ciki musamman a fagen ci gaban kasa, shugaba Trump ya bayyana cewar: Amurka ta kashe kimanin Dala Triliyon 6 a yankin Gabas ta tsakiya alhali kuwa tubalin ci gaban kasarmu na cikin tsaka mai wuya. Da wadannan dala triliyon 6 za mu iya sake gina kasarmu har sau biyu, kai watakila ma har sau uku idan muna da mutanen da suka iya tattaunawa.
A yayin wannan jawabin dai, Trump yayi kokarin wajen bayanin taken da yayi amfani da shi yayin yakin neman zabe ga 'yan majalisar da kuma miliyoyin Amurkawa da suke kallonsa shi ne batun sake dawo wa Amurka da mutumcinta wanda ya ce ta rasa shi tsawon shekarun da suka gabata.
To sai da dama daga cikin masana suna ganin wasu daga cikin wadannan alkawurra, wasu batutuwa ne da ba za a iya tabbatar da su ba, ko kuma idan ma har za a tabbatar da su din to ba a nan kusa ba. Ga misali batun kawar da talauci da amfani da muggan kwayoyi, rashin aikin yi, amfani da karfi da rashin tsaro, dukkanin wadannan wasu abubuwa ne da al'ummar Amurka take fama da su wadanda kawar da su ba abu ne mai sauki ba musamman a cikin irin halin da Amurkan take ciki.
Haka nan kuma idan muka koma ga batun da yake yi na sake gina tushen ci gaban Amurkan don haka ne ma yake cewa shi shugaban Amurka ne ba shugaban duniya ba, to amma a bangare guda kuma yana magana kara kasafin kudin soji da kuma kafa mafi karfin sojoji a tarihin Amurka. Ko kuma batun da yake yi na tsayawa kyam tare da kawayen Amurkan a kungiyar NATO da kuma ci gaba da goyon bayan 'Isra'ila' ido rufe kamar yadda sauran gwamnatocin jam'iyyar Republican na Amurkan suke yi, bugu da kari kan zaban mashawarta da jami'an gwamnatin da suke da irin wannan akida, dukkanin wadannan abubuwa ne da suke nuni da akidar son yaki da kuma wuce gona da iri kan wasu kasashe wadanda su ne ummul aba'isin din tsaka mai wuyan da Amurkan take ciki a halin yanzu musamman a yankin Gabas ta tsakiyan sakamakon farkawar da al'ummomin yankin suka yi da kuma kin amincewa da mulkin mallakan Amurka da kawayenta.
A saboda haka ne wasu masanan suke ganin wannan jawabi na Trump, bai wuce kawai maganganu na fatar baki amma dai daga dukkan alamu ba ta sauya zani ba.