Malaysia Ta Kori Jakadan Koriya Ta Arewa
Kasar Malaysia ta sanar da korar jakadan Koriya ta Arewa daga kasarta, a daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu bayan kisan dan uwan shugaba Kim Jong-Un a filin jirgin saman Kuala Lampur.
Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen ta Malaysia ta ce daga jiya Asabar jakadan na Koriya ta Arewa ba shi da wani matsayi a kasar.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kasar ta Malaysia ta bukaci shugaba Kim Jong-Un ya nemi gafara a gare ta saboka kalamensa na cacakar hukumomin kasar akan binciken da suke kan kisan dan uwansa Kim Jong-Nam.
Ko baya ga wannan matakin Malaysia ta ce daga ranar 6 ga watan Maris ta dakatar da yarjejeniyar dake tsakanin kasashen biyu ta shige da fice ba tare da takardar visa ba.