Amurka : Trump Ya Sanya Hannu Akan Sabuwar Dokar Baki
Shugaba Donald Trump na Amurka, ya sanya hannu kan wata sabuwar doka data shafi baki, bayan da wata kotun kasar tayi watsi da wacen makamanciyarta data tanadi hana baki daga wasu kasashen musulmi bakwai shiga kasar.
A Ranar 16 ga watan Maris din nan ne sabuwar dokar zata fara aiki a cewar mashawarciyar shugaban kasar, Kellyanne Conway a gidan talabijin din Fox News.
Misis Conway, ta ce an samu sauyi a cikin sabuwar dokar inda aka cire Iraki daga cikin kasashen da dokar ta shafa, saboda hadin kan data bayar wajen bada bayyanan da ake bukata, aman matakin na nan daram akan sauren kasahen shida.
Haka zalika kuma a cewar jami'ar sauren baki da suke zaune Amurka masu takardar visa da katin zama kasar zasu samu kariya daga sabuwar dokar, kuma suma 'yan gudun hijira Syria zasu samu sukuni a wannan sabuwar dokar.
Idan ana tune wacen dokar ta farko da Trump ya sanyawa hannu a ranar 27 ga watan Janairu ta tanadi hana baki da kuma musulman wasu kasashe bakwai sanya kafa Amurkar, kafin daga bisani wani alkalin kotun tarayya yayi wasti da ita.