Bakin Haure Suna Ci Gaba Da Halaka A Tekun Mediterranea
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18310-bakin_haure_suna_ci_gaba_da_halaka_a_tekun_mediterranea
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Bakin haure da suke kokarin tsallakawa zuwa kasashen yammacin Turai ta hanyar teku suna ci gaba da rasa rayukansu musamman a tekun Mediterranea.
(last modified 2018-08-22T06:59:47+00:00 )
Mar 07, 2017 14:11 UTC
  • Bakin Haure Suna Ci Gaba Da Halaka A Tekun Mediterranea

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Bakin haure da suke kokarin tsallakawa zuwa kasashen yammacin Turai ta hanyar teku suna ci gaba da rasa rayukansu musamman a tekun Mediterranea.

Majalisar Dinkin Duniya a yau Talata ta fitar da sanarwar cewa: Bakin hauren da suka halaka a tekun Mediterranea a kokarin da suke yi na tsallakawa zuwa kasashen yammacin Turai daga farkon wannan shekara ta 2017 zuwa ranar 5 ga wannan wata ma Maris sun kai kimanin 521.Yayin da yawan bakin hauren da suka mutu a tekun na mediterranea a shekarar da ta gabata ta 2016 a tsawon wannan lokacin suka kai 471.

Majiyar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa: Bakin hauren da suke shiga cikin kasashen yammacin Turai, mafi yawansu suna tsallakawa ne cikin kasar Italiya ta kasar Libiya, inda kimanin 19,348 da suka shiga cikin kasashen na Turai kashi 80 cikin dari suna cikin kasar Italiya ce sakamakon haka gwamnatin kasar ta kulla wata yarjejeniya da bangaren kasar Libiya kan taka burki wa bakin hauren ta hanyar tsaurara matakan tsaro a gabar tekun kasar ta Libiya.