Damuwar MDD kan tsanatar hare-haren ta'addanci a Somaliya
Wakilin MDD a kasar Somaliya ya yi alawadai kan harin Bam din da aka a kasar
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Manzon musaman na MDD kan Kasar Somaliya na yin Alawadai da wasu tagwayen harin Bom din da aka kai kasar wanda ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar Mutane da dama.
Jami'in ya ce halin da kasar ke ciki musaman matsalar fari da ya janyo matsalar karamcin abinci,kuma ga irin wannan hari na ta'addanci zai kara jefa kasar cikin mawuyacin hali.
Majiyar Asibi da ta jami'an tsaro sun sanar da cewa a jiya Litinin wasu Motoci biyu shake da bama-bamai sun tarwatse a kusa da wani Otel dake kan babbar hanya ta birnin Magadushu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 8 tare da jikkata wasu 7 na daban.
Har ila yau a jiya Litinin Jami'an 'yan sanda sun buda wuta kan wata Bas, bayan da umarci direban Motan ya tsaye, ya ki tsayawa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa tare da jikkata wasu fararen hula guda biyu.