Amurka : Gwamnatin Trump Ta Daukaka Kara Kan Soke Dokar Baki
Gwamnatin shugaba Donald Trump na Amurka ta daukaka kara kan sokewar da wani alkalin kotun tarayya na yankin Maryland ya yiwa sabuwar dokar hana 'yan gudun hijira da musulmin wasu kasashe shida shiga kasar.
Yanzu dai za'a mika dokar ga wata kotu dake birnin Richmond na Virginia.
A ranar Alhamis ne alkalin mai suna heodore Chuang ya soke dokar ta wani dan lokaci saboda yadda dokar ta shafi hana bayar da takardar izinin shiga kasar Visa
) da kuma hana wasu kasashen musulmi shida shiga kasar.
Alkalin dai ya ec sabuwar dokar na kara tabbatar da kallamen da Donald Trump ya yi a lokaci yakin neman zabensa na hana musulmi sanya kafa a kasar.
Dama kafin hakan wani alkalin kotun tarayya Hawaii ya soke dokar wace ya ce ta nuna wariya ce da kyammar musulinci.