Dala Miliyan 75 Don Kare Wurare Masu Tarihi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18672-dala_miliyan_75_don_kare_wurare_masu_tarihi
Wasu Kasashen duniya Bakwai da masu bada tallafi sun alkawarta samar da Dala Miliyan 75 na Amurka domin kare wurare masu tarihi dake fuskantar barazana yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda, musamen a yankin Gabas ta tsakiya.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 20, 2017 13:38 UTC
  • Dala Miliyan 75 Don Kare Wurare Masu Tarihi

Wasu Kasashen duniya Bakwai da masu bada tallafi sun alkawarta samar da Dala Miliyan 75 na Amurka domin kare wurare masu tarihi dake fuskantar barazana yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda, musamen a yankin Gabas ta tsakiya.

Yau kusan shekara biyu da suka wuce da aka gabatar da wannan shiri wanda ke da gurin bayyana yadda kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ke lalata wurare masu tarihi.

Tun dai bayan da hukumar kula da wurare masu tarihi ta MDD (UNESCO) ta gabatar da jawabi a taron kashen G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya shirin ya fara kankama.

Kasashen bakwai da suka hada da faransa, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da masu bada tallafi da kuma hukumar UNESCO na son kafa asusun Dala Miliyan 100 kafin nan da shekara 2019, wanda tuni aka samu kashi uku cikin hudu na kudaden.