Ci gaba da cin zarafin Musulmi a Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18724-ci_gaba_da_cin_zarafin_musulmi_a_amurka
Al'ummar musulmi a Jihar Lowa ta kasar Amurka sun bukaci a gudanar da bincike kan wasikar da aka aika musu ta barazana.
(last modified 2018-08-22T06:59:51+00:00 )
Mar 22, 2017 07:53 UTC
  • Ci gaba da cin zarafin Musulmi a Amurka

Al'ummar musulmi a Jihar Lowa ta kasar Amurka sun bukaci a gudanar da bincike kan wasikar da aka aika musu ta barazana.

tashar telbijin Press Tv dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa Cibiyar musulci ta kasar Amurka Des Moines ta samu wata wasika inda a cikin ta aka rubuta cewa sabon Shugaban kasar Amurka Donal Trump zai yi mu'amala da musulmi kamar yadda Hitler ya yi da Yahudawa.

Wasikar da wani gungu na Amurkawa da ake kira Amurkawa domin hanya mafi inganci suka sanyawa hanu,an ci zarafin musulmi sosai a cikin ta.

A cewar Dakta Samir Shamsh Shugaban kungiyar musulinci ta Des Moines, halin da musulmi ke ciki a kasar ta kai wasu na tsoron tura 'ya'yansu makaranta, wasu kuma ma sun fasa sanya hijabi kuma sun yi ban kwana da masallatai.

Alkaluma sun tabbatar da cewa daga lokacin da Shugaba Trump ya lashe zabe, cin zarafin da ake yiwa al'umar musulmi a kasar Amurka ya karu sosai.