Majalisar Dokokin Canada ta amince da dokar kalubalantar masu kyamar musulinci
Majalisar Dokokin Canada ta amince da kudirin da Piraministan kasar ya gabatar na daukan mataki da zai kalubanci masu kyamar addinin musulinci a kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta a jiya Alkhamis Majalisar Dokokin kasar Canada ta amince da wani gudiri da Piraminista Justin Trudeau na kasar ya gabatar na daukan mataki kan matsalolin masu kyamar addinin Islama, har ila yau Majalisar ta bukaci Gwamnati da ta dauki kwararen mataki a kan masu gyamar addini a kasar.
Bisa wannan sabon kudiri, Gwamnatin kasar ta Canada za ta gudanar da bincike domin gano da kuma kalubalantar duk wanda aka samu yana kyamar wani addini a kasar musaman ma masu gyamar addinin Islama.
Wannan matakin na zuwa ne bayan harin da wasu masu kyamar addinin Islama suka kai wani masallaci a kasar inda kashe 6 daga cikin masallata.ko baya ga wannan a cikin 'yan watanin nan an kai hare-hare da dama cikin Masallatai a yankuna daban daban na kasar.