Rasha : Putin Ya Gana Da Marine Le Pen
-
\\\'Yar takara jam\\\'iyyar FN, Marine le Pen da shugaba Vladimir Putine na Rasha
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gana da 'yar takara shugaban kasar Faransa mai tsananin ra'ayin rikau, Marine le Pen.
Wannan dai shi ne karon farko da Mista Putin ya gana da 'yar takarar, tare da jaddada cewa hakan baya nufin Rasha na shishigi a cikin harkokin zaben kasar ta Faransa na watan gobe.
Ba kasafai ne ba dai shugaba Putin ke yin irin wannan alfarma ga 'yan takara zaben shugaban wata kasa.
Ganawa da wani shugaban kasa mai karfin fada a ji a duniya kamar Rasha, ba karama nasara ce ba ga Marine le Pen, a kasa da wata guda na zaben shugabancin kasar ta Faransa.
'Yar takara jam'iyyar ta FN dai na adawa da takunkumin da kungiyar tarayya Turai ta kakabawa Rasha akan mamayar yankin Krimiya.
Kafin Vladimir Putin, 'yar takarar Marine le Pen ta gana da shugaban kasar Labanon Michel Aoun da kuma shugaba Idriss Deby na Chadi.